Shugaban rukunin gidajen gonar Nana Farm limited Alhaji Muhammad Aminu Adamu Abba Boss ne ya bayyana hakan cikin shirin Abokin Tafiya na mujallar Matashiya.
Boss ya ce duba ga yadda aka rufe iyakokin ƙasar nan ba tare da ana shigo da komai ba, hakan zai sa ƴan Najeriya su lasru ga abubuwan da akae sarrafawa a gida wanda aka tabbatar da ingancinsa.
Abba Boss ya ƙara da cewa da yawan abinci da ake shigo da su daga ƙasashen ƙetare sai an musu feshin magani don kar su lalace wanda hakan ke sa a kamu da cututtuka har ma suka addabi al umma.
Boss ya ƙara da cewa batun tsadar kaji da aketa kokawa kuwa, abu ne da har yanzu suke ƙoƙarin wadata al umma nan ba da jimawa ba, amma ya tabbatar da cewar nan gaba kaɗan jama a sza su samu wadataccen kwai da kuma naman kaji a sauƙaƙe.
Shirin Abokin Tafiya dai ana gabatar da shi ne a shafin mujallar Matashiya da ke YouTube 16 ga kowanne wata.