Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta yi sammacin mawallafin mujallar Matashiya bisa wani rahoto da ya wallafa.

An yi sammacin Alhaji Abubakar Murtala Ibrahim ne bayan wallafa wani rahoto da ya yi a ranar 7 ga watan Oktoba 2019 wanda wani malami ya yi fatawa kan yin wasan Hausa da waƙa.
An gayyaci mawallafin mujallar Matashiya zuwa helkwatar ƴan sanda da ke Kano don amsa tambayoyi dangane da rahoton da ya wallafa.

Cikin wani shirin talabiji da ake sakawa a shafin mujallar Matashiya na YouTube mai suna Rabin Ilimi wanda wani ya aiko da tambaya shin ya halatta a yi wasan Hausa da waƙa?

Babban Malami a hukumar Hizbah ta jihar Kano Shek Muhammad Tukur Moriki R/Lemo ke amsa tambayoyin a shirin kuma ya amsa da cewa “E ya halatta matuƙar za su ƙarfafi musulunci da musulmi, kuma waƙar da aka yita babu ƙarya ko ziga a cikinta domin zamanin sahabbai ma an yi haka zalika wasan Hausa ma ya halatta matuƙar akwai faɗakarwar da ta yi daidai da addinin musulunci”. inji shek Moriki.
A ƙoƙarin yin amfani da damar da ta bawa ɗan jarida dama na yin salo na jan haɓkalin jama a don karkata zuwa karanta labarin ne kuma aka rubuta “Fim da waƙa halak ne kuma jihadi ne masu na samun ɗumbin lada mara iyaka”
Wannan dai salo ne da doka ta bawa ɗan jarida dama don jan hankalin mai karatu zuwa karanta labari ko rahoton da ya wallafa.
A bisa daidaiton kalamai da furucin shek kuwa idan muka kalli amsar da ya bayar na halaccin da kuma nuni da cewa zai taimaki musulunci da musulmi to kuwa tamkar jihadi ne, kamar yadda ya tabbata cewa duk abinda mutum zai yi matuƙar zai taimaki addini ya halatta kuma jihadi ne sannan duk wanda ya yi jihadi zai samu lada mai yawa.
Bayan wallafawar ne kuma abokan aiki suka ɗauki labarin inda wata jaridar yanar gizo ta wallafa, sai dai a wancen shafi Mallam ya sha zagi ganin waɗan suka yi zagin da alama ba su karanta gundarin labarin ba.
Da ganin haka mallam Muhammad Tukur Moriki ya kira Abubakar tare da sanar da shi halin da ake ciki, ganin damuwa da mallam ya shiga nan take aka gyara kanun labaran kamar yadda mallam ya buƙata don hankalinsa ya kwanta, an mayar da kanun labaran kamar haka ” Fim da waƙa halak ne kuma jihadi ne idan an bi tsarin musulunci masu yi za su samu ɗumbin lada mara iyaka -Shek Moriki”
Kuma Abubakar ya umarci wanda suka ɗauki labarin da su gyara kamar yadda aka gyara.
Haka kuma bayan nan aka yi saboda labari da aka masa kanun kamar haka ” Duk wasan Hausa ko waƙar da ba zai taimaki musulunci da musulmi ba haramun ne – Shek Moriki”
kuma a ciki an yi bayani cikakke ga waɗanda ke kallin shehin malamin ta wata fuska daban.
Haka kuma aka naɗi muryar mallam wamda aka yi amfani da ita a kafar yaɗa labarai ta rediyo wanda yake bartanta kansa da waccen kalma.
Bayan kammala duk waɗancan matakai ne kuma Dalilin da mallam ke ganin an ɓata masa suna ya kamata ya ɗauki mataki na shari a har ya kai ƙorafi ga jami an ƴan sanda, bayan da ta tabbata cewa idan ma laifi ne to daga mujallar Matashiya ne kuma wanda ya wallafa shi ya yi, sai mallam ya yi ƙoƙarin janye ƙarar har ma ya tabbatar da cewa ko Abubakar ba zai taɓa ɓata masa suna ba.
Amma duk da haka sai da aka sa mawallafin mujallar Matashiya Abubakar Murtala Ibrahim sake sabon rubutu fil kuma aka karanta ga mallam ya tabbatar an wankeshi an ɗora laifin ga mujallar Matashiya sannan aka karanta masa ya gamsu sai aka wallafa, kuma aka umarci wancen ɓangare da suma su wallafa a shafinsu.
A ranar Talata 29/10/02019 ne Mawallafin mujallar Matashiya Abubakar Murtala Ibrahim ya amsa gayyatar ƴan samdan da misalin ƙarfe 12pm na rana kamar yadda suka gayyaceshi, kuma suka shafe sama da awanni biyar a helkwatar ƴan sanda da ke Bompai a Kano.
Za mu saka cikakken shirin a gobe da misalin ƙarfe 8:30pm na dare.