Kotun daukaka kara da ke zama a Kaduna ta soke zaben dan majalisar tarayya mai wakiltar Tudun Wada/Doguwa Alasan Ado Doguwa.

Alasan Ado Doguwa wanda shi ne shugaban masu rinjaye na majalisar tarayya wato mai mukami na uku a majalisar bayan shugaban majalisar da mataimakinsa.
kotun ta bayyana zaben a matsayin mara inganci, Mai shari’a Justice Oludotun Adefope-Okojie, ya ce bayyana Doguwa a matsayin wanda ya lashe zabe ba zai yiwu ba, domin hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC ta cire sunayen wadansu jam’iyyun a yayin ayyana sakamakon zaben. Haka kuma kotun ta ce INEC ta karya doka ta hanyar rubuta sakamakon zaben jam’iyya biyu kawai cikin 53 da suka shiga zaben a fom mai lamba 0EC 8 (II) E.

Kuma saboda haka kotu ta nemi INEC ta sake shirya wani zaben nan da kwana 90 a yankin.
