Mai riko da mukamin shugabancin hukumar dake Biyan Albashi da hakkunan Ma’aikatan Najeriya Ekpo Nta,
Yayi alkawarin karawa yan fansho kudin da ake basu na fansho muddin kungiyar kwadago ta cimma matsaya da gwamnati kan sabon tsarin Albashi mafi karanci dubu talatin.

Nta ya bayyana hakan ne a lokacin da Shugaban kungiyar Yan fansho na kasa Abel Afolayan ya kawo masa ziyara a ofishinsa dake Abuja.
Afolayan yace wanann ba karamin farin ciki zaiyi ba idan hakan ya tabbata kasancewar a Najeriya akwai Yan fansho da har yanzu Dubu biyu ake basu a matsayin kudin fanshonsu mafi yawa kuwa dubu Goma ne kuma dashi suka dogara.

