Jami’an tsaron filin tashi da saukan jirage na Aminu Kano dake jihar kano sun cafke wata mata Mai matsakaicin shekaru da suke zargin ta sato Jaririya yar watanni Shida da haihuwa.

Jami’an dai sun cafke matan ne da take Kokarin hawa jirgin sama na Azman zuwa jihar Legas.
Tuni dai jami’an suka Mika matar Hannun jami’an yansandan filin Jirgin saman don cigaba da bincikar matar.

Kamar yadda kafar yada labarai ta Solacebase suka rawaito
