Gwamnatin jihar zamfara tace kasar Amurka ta cire sunan zamfara cikin garuruwan Yan ta da kayar baya a Najeriya.

Gwamnan jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle shine ya bayyana hakan a gaban dubban Magoya bayan jam’iyar APC a Karamar hukumar Maradun.
A cewar gwamnan jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin da kasar Amurka ta hana mutanenta zuwa.

Sai gashi a satin da ya gabata gwamnatin Amurka ta cire sunan zamfara daga cikin jihohi masu Hadari a Najeriya.

Wannan ya biyo bayan irin Kokarin da Wannan gwamnatin tayi na dakile Yan Ta da kayar baya da masu garkuwa da Mutane a jihar.