Jami’an dake yaki da masu fataucin miyagun kwayoyi NDLEA sun yi nasarar cafke wani jami’in Soja da yake safarar miyagun kwayoyi da yake kaiwa Yan kungiyar Boko Haram.

Jami’an da ba’a bayyana sunansa ba an kamashi ne da haramtaccen kwayoyi na Tramadol mai nauyin Kilogram 59 inda yake Shirin shiga Garin Gwoza na jihar Borno.

Kwamandan hukumar NDLEA Na jihar Yobe Reuben Apeh shine ya shaida hakan ga manema labarai a Garin Damaturu inda yace an cafke shine a ranar 7 ga watan Nuwamba.

Yanzu haka yana hannu inda ake cigaba da bincike akansa.

Bayan da Wanda ake zargin ta bayyana cewa shima wani jami’in kwastam ne yake siyar masa cikin kwayoyin da suka kwace a jihar Legas.

Leave a Reply

%d bloggers like this: