Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mutawalle ya bayyana cewa muddin aka sake kai hari a jihar Zamfara to sai ya kama tsohon gwamna Abdulaziz Yari.

Gwamnan ya kara da cewa, wannan shine karo na uku da aka samu rashin zaman lafiya yayin da tsohon gwamnan ya ke zuwa jihar.

A cewar Matawalle“Nasarata a matsayin gwamnan jihar da kuma nasarar kawo zaman lafiya dalumana duk Allah ne ya rubuta.
Ba zan bar tsohon gwamnan da mutanen sa su lalata min kokarin da nake yi ba.a.jihar Zamfara”

Ya kuma kara da cewa “Daga yanzu, zai fara nuna ikon jihar Zamfara a hannun sa yake ba a hannun tsohon gwamnan ba.
Kuma zamu yi amfani dashi don cigaban mu tare da kare miliyoyin al’ummar jihar Zamfara,” Inji gwamna Matawalle.
Kamar yadda Muryar yanci ta Rawaito.

Leave a Reply

%d bloggers like this: