Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa sakamakon rufe iyakokin Najeriya yanzu haka ta kama kaya da kudinsu ya Kai biliyan 3.5.

Ministan yada labarai da Al’adu Alhaji Lai Mohammad ne ya bayyana hakan a lokacin da ya Kai ziyara garin Seme Border iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin.
Kamfanin dillancin labarai ta rawaito cewa lai Mohammad na daya daga cikin ministoci masu rangadi kan rufe iyakokin da akayi Wanda Suka hada da Ministan Al’amuran cikin gida Rauf Aregbesola da na kasashen waje Goefrey onyeama sak karamin ministan kudi Clement Agba.

