Babbar kotun Tarayya dake Maitama Abuja ta ayyana 27- janairu, 2020 ne ranar da zata yanke hukunci akan maryam Sanda, wacce ake zarginta da kashe mijinta Bilyaminu Bello da gangan.

Tun bayan sauraren shaidun dukkanin bangarori da shawarwari, Mai shari’a Yusuf Halilu ya tsayar da ranar 27/Jan/2020 Ranar yanke hukunci na karshe.
Tun a shekarar 2017 Yan Sanda suka gurfanar da Maryam Sanda gaban kotu bisa zargin kashe Mijinta.

Ana dai tsare da Maryam Sanda ne tare da Dan Uwanta, Aliyu Sanda, da mahaifiyarta Maimuna Aliyu, Sai Mai aikinta Sadiya Aminu.
