Ƙungiyar ƴan Adaidaita sahu ta jihar Kano ta bayyana jingine tsunduma yajin aikin da ta shirya yi a gobe Juma a.

Shugaban masu tuƙa Adaidaita sahu na jihar Kano Alhaji Sani Sa id Ɗankoli ne ya bayyana hakan bayan wani zama da sukai da ɓangaren gwamnati.

Ya ce sun cimma matsayar biyan kuɗi naira dubu takwas na na urar da za a maƙala a babur ɗin, daga bisani kuma a biya sauran kuɗaɗen maimakon biya a lokaci guda.

A nsu ɓangaren shugaban hukumar kula da tuƙi a jihar Kano KAROTA Alhaji Baffa Babba Ɗanagundi ya ce sun samu matsayar raba kuɗin maimakon bayarwa a lokaci ɗaya, za a fara biyan naira dubu takwas daga bisani zuwa ƙarshen watan Disambar shekarar nan a biya sauran kuɗaɗen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: