Gwamna jihar Nassarawa Alhaji Abdullahi Sule ya tabbatar da cewar zai gina katafariyar tashar mota ta zamani don rage cunkoson ababen hawa.

Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana hakan ne yayin wani taro da ya yi da masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumar Karu.

Ya ce gina tashar zai taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa musamman masu tafiye tafiye daga Keffi zuwa Abuja, sannan hakan zai taimaka wajen shawo kan matsalar tsaro a jihar.

Tashar motar za ta kasance wadda za ɗauki aƙalla motoci 900 da gidajen kwanan direbobi, gidan abinci, banɗakuna da kuma gidan mai.

Da yawa daga cikin masu ruwa da tsaki ne suka halarci taron har ma da wasu daga cikin ƙungiyoyin masu zirga zirgar ababen hawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: