Shugaban mujallar Matashiya Abubakar Murtala Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin da yake buɗe sabon kamfanin tallace tallace na hanyoyin sadarwar zamani wato BIG TAKE a ƙaramar hukumar fagge a Kano.

Ya ce samun matasa jajirtattu maau amfani da fasaharsu zai taimaka wajen wadatar samun aikin yi da ake fama da shi a ƙasa.
Hoton Bayan buɗe kamfanin

Kamfanin wanda ɗaya Alhaji Babangida Aminu ke jagoranta kuma ya kasance daga cikin waɗanda suka amfana da koyon sana a kyauta da mujallar Matashiya.

“Wannan bain alfahari ne a garemu kuma muna fata hakan ya zama abin koyi ga sauran matasa ta yadda za su ke dogaro da kansu.
“Duniya ta cigaba ne da haka kuma kowacce ƙasa na alfahari da matasa musamman masu kwazo wajen ƙirƙirarwa kansu abin yi don taimakon kansu da sauran ƴan uwansu matasa kuma hakan zai taimawa tattalin arziƙin ƙasa” a cewar Abubakar.
Sannan ya ja hankalin matasa da su kasance masu haƙuri tare da jajircewa a kan abinda auka sa a gaba don kaiwa ga gaci.
Kafin buɗe kamfanin
A nasa jawabin shugaban kamfanin BIG TAKE Alhaji Babangida Aminu ya yi godiya ga Allah da ya sa suka kai ga wannan mataki, sannan ya shawarci sauran matasa da su yi haƙuri a duk yanayin da suka tsinci kansu muddin suna kan hanya ta kwarai.
Sannan ya yi gidiya ga mujallar Matashiya ganin yadda suka ƙara masa kwarin gwiwar aiwatar da hakan kasancewarsa ɗaya daga cikin ɗaliban da suka koyi sana ar ɗaukar hoto mara motsi da mai motsi wato bidiyo kuma kyauta.
An ƙaddamar da Kamfanin ne a yau Laraba 1/1/2020 kuma shugaban mujallar Mataahiya Abubakar Murtala Ibrahim ne ya buɗe wajen.
Ayyukan da za a ke gudanarwa a kamfanin sun haɗar da tallace tallace ta hanyoyin sadarwar zamani da ma shirye shirye na kallo wato talabiji.