Gwamnatin jihar borno ta raba kayan abinci ga wadanda harin boko haram ya rutsa da su har suka bar gidajesu a jihar Borno.
Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum ya ziyarci wajen rabon kayan abincin wanda aka bawa yan asalin jihar wadanda suka rasa muhallinsu.
Babagana Umara Zulum ya raba kayan abinci da suka hada da masa, da shinkafa, wake, man girki da sauransu har ma da kudin cefane.
Mutane akalla dubu goma sha shida ne suka amfana da wannan tallafi a garin gwoza, garin da yan kungiyar book haram suka taba rikewa a baya.
Sannan ya dauki tawon kwanaki uku don ganewa idonsa yadda rabon kayan abincin ke gudana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: