Rundunar ƴansandan jihar Kogi sun ceto wani Mohammed Salisu Cache,  Abdulrazaq Mohammed da kuma Abdulraq Anataku waɗanda ƴan bindiiga suka yi garkuwa da su tun a watan Disamban shekarar da ta gabata.

Mai magana da yawun rundunar William Aya ya ce mutane ukun da aka yi garkuwa da su lamarin ya faru ne lokacin da suke kan hanyar dawowa daga tafiya ne ƴan bindigan suka buɗe musu wuta har ma suka kashe mutum ɗaya daga ciki.

Ya ce an ceto mutum ukun ne bayan da jami an ƴan sandan sashe na musamman don yaƙi da ƴan fashi da makami da kuma ƴan sanda masu kwatar da tarzoma suka bazu cikin dajin da ya zamtomaɓoyar ƴan bindigan.

Kuma za su cigaba da haɗa kai da dukkanin jami an tsaro don yaƙar ɗabi ar a faɗin jihar a cewar kwamishinan ƴan sandan jiharMista Ede Ekpeji.

Leave a Reply

%d bloggers like this: