Gwamnatin jihar katsina ta shirya yiwa yara Akalla Miliyan biyu Allurar Riga-kafin shan Inna tun daga 11 ga watan janairu zuwa 14 na shekarar 2020.

Sakataren hukumar lafiya Matakin farko na jihar Dr Shamsu yahaya shine ya bayyana hakan a lokacin da yake Tattaunawa da manema labarai a jiya lahadi.
Inda yace hukumar sa ta shirya tsaf na ganin anfara wannan Allurar Riga-kafin inda ya tabbatar da cewa yaran da aka haifa jarirai zuwa Yan Watanni hamsin da tara ne za’ayi musu Allurar a fadin kananan hukumomi 34 na jihar katsina.

