Daga Jamilu lawan yakasai

Rahoton da mujallar matashiya ke samu na nuni da cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane sun awon gaba da matar wani Dan majalisa a jahar jigawa dake najeriya
Yanbindiga sunyi garkuwa da matar danmajalisa haruna aliyu dake wakiltar miga acikin jahar jigawa.
Mai magana da yawun rundunar ‘yansanda rashen jahar DSP Abdu Jinjiri ya shaidawa BBC cewar wasu ‘yanbindaga su ukune suka shiga harcikin gidan danmajalisar inda sukayi garkuwar da matar danmajalisar mai suna Zahra’u Aliyu.
Yace yan bindigar basu karbi kudi ba yayin da suka shiga gidan.
Ya kuma ce yanbindigar sunshiga gidan shi ne da misalin karfe 5:00 na asubahi wayewar garin ranar Asabar.
Matsalar garkuwa dai nakara habbaka ajahar jigawa inda acikin ‘yankwanakinnan ake garkuwa da iyalen manyan jami’an gwamnati.

