Ba Ruwa
Ba Hanya
Ba Makaranta
Ba Asibiti

Da sunan Allah mai Rahma mai jin ƙai
Wasiƙa zan aike zuwa ga lamba ɗaya a Kano Mai girma Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje
Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan ana cigaba da ƙoƙarin samar da mafutar al umma kamar yadda aka zaɓeka a matsayinka na gwamna.
Muhimman abubuwa nake tafe da su kan wani yanayi da mutanen wani yanki a tsakiyar inda kake mulka suke fama kuma na san kowanne shugaba abinda zai fi maida hankali a kan shugabancinsa bai wuce ganin ya samawa al ummarsa waɗannan gwala gwalan madafun gudanar da rayuwa ba.
Mai girma gwamna ta yuwu ka sani ba mamaki kuma baka san halin da mutanen nan suke ciki ba, magana nake a kan al ummar unguwar da ta haɗa da Rimin Kebe, Dausara, Ƴar Adua Kwatas, Zangon Marikita, Faƙo da sauransu.
Mai girma gwamna duk da cewar na san ka shiga yankinnan kuma ka ga yanayin da suke ciki tun lokacin kamfen ɗin zaɓen da ya gabata musamman abinda kowa ya shiga zai bada tabbacin gani da ido wato matsalar hanya.
Mai girma gwamna waɗannan mutane da suke rayuwa a wannan tsuburi talakawanka ne, a ƙasanka suke, kai suke kallo a matsayin mai jiɓantar lamarinsu.
Gwamna Khadimul Islama kana da labarin a wannan tsibiri babu makarantar sakandire ko ɗaya a ciki? Kana da labarin babu asibitin kwanciya kaf wannan gari? Ko kuwa kana da labarin ba su ma san menene ruwan sha na famfo a waɗannan yanki ba? Ga matsalar rashin titin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a wannan yanki.
Mai girma gwamna cikin ladabi nake kiran sunanka tare da bayyana maka cewar a wannan yanki akwai miliyoyin mutane kuma na san ka san da haka.
Ta yaya za su gane cewa suma ana mulkin damokaraɗiyya kuma za su mora? Wanne abu za a musu don a amfanar da su daɗin gwamnatinka, mai girma gwamna ilimi shi ne ginshiƙi na rayuwa kuma shi yake saita yara su zamto manya na gari ,idan aka ɓarsu cikin wannan yanayi waɗanne irin matasa kake gani za a samar a gobe?
Tare dadukkan girmamawa ina mai kira da babbar murya a kan cewa ya kamata a duba halin da mutanen nan suke ciki.
Na san cewar kowanne shugaba burinsa daɗaɗawa mutanen da yake mulka kuma ina maka kyakkyawan zaton haka.
Mai girma gwamna idan fa damuna ta faɗi mutanen wannan yanki na shiga mummunan yanayin da ko masu ababen hawa na haya ba sa shiga yankin
Akwai bidiyon mummunan yanayin da na san ba za ka so a wallafa ba saboda hakan zai zamto tamkar naƙasu a gwamnatinka.
Mai girma gwamna hatta ziyara mutane ba sa ƙaunar shiga wannan yanki, ƴaƴanka ƴan mata na wannan unguwa sun rasa samarinsu da dama a kan wannan matsala.
Duk da kasancewar akwai mutane da suke da kishin karatu a wannan yankin ma tabbatar aka samar da ko da makarantar sakandire ce guda ɗaya tak za a magance wasu matsalolin da dama.
Abubuwan da yawa amma wannan tamkar saka ɗamba ne a kan lamuran al umma kuma ina fata saƙon zai riskeka ba tare da kallon rubutun da wata fuskar ba.
Abubakar Murtala Ibrahim
19 Jumada Ula 1441
14/1/2020

