Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya amince da naɗin Baba Sharif Dala a matsayin kwamishinan yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar kano.

Gwamnan ya amince da naɗin bayan dama da kunɗin tsarin mulki ya bawa gwamnati dama don naɗa kwamishinoni biyu masu cikakken iko tare da ƙarin wasu biyun na wucin gadi.

An naɗa Baba Sharif Dala a matsayin kwamishina mai cikakken iko kuma za a miƙa sunansa gaban majalisa don tantancewa kamar yadda doka ta tanada.

Leave a Reply

%d bloggers like this: