Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta sake bankaɗo asirin wani gida a unguwar sabon gari wanda wani inyamuri da matarsa ake zargi suna ajiye yara waɗanda aka sato da sunan gidan marayu ba tare da izini ko sanin gwamnati ba.
Aƙalla yara 19 rundunar ta kuɓutar a wani gida da ke sabon gari wanda ake ajiye yaran da sunan gidan marayu.

Haka kuma hukumar sun bi diddigin wani gida a Kaduna wanda ke haɗa baki da wani mai asibiti da ake kai musu jarirai da zarar an haifeshi.

Kakakin hukumar DSP Abdullahi Kiyawa ya tabbayar mana da cewar tuni wanda mai asibitin ya tsere ya bar ƙasar.
Runsunar ta bada sanarwar duk wanda ya san an sace ɗansa da ya hanzarta zuwa helkwatar ko Allah zai sa a dace.

A yayin da yake holen masu laifikan kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Habu Ahmad Sani ta bakin kakakin hukumar DSP Abdullahi Haruna ya ce rundunar ta kama masu laifuka daban daban da suka haɗar da satar mutane, fashi da makami, kwacen waya da wani wanda ke siyar da madarar da wa adinta ya ƙare.

DSP Abdullahi Haruna ya ƙara jaddada aniyar ƴan sanda na yaƙar dukkan ɗabi ar ɓata gari.

Cikin wasu da mujallar Matashiya ta zanta da su sun nuna nadamarsu dangane da laifin da ake zarginsu da aikatawa

Mutane fiye da 200 rundunar da kama waɗanda ake zargi da aikata laifuka daban daban kamar satar motoci da babura, safarar kayan maye da dai sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: