Cikin jawabinsa, jim kaɗan bayan tabbatar masa da nasara a kotun ƙoli gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana godiyarsa ga Allah da kuma al ummar Kano bisa nasarar da ya samu.

A wata sanarwa da babban sakataren watsa labaran gwamnan Kano Mallam Abba Anwar ya fitar, gwamna GandujeYa ce a shirye yake don tafiya da ƴan jam iyyar adawa don cigaban Kano da Al ummar jihar Kano.

Gwamna Ganduje ya samu nasara bayan da kƙtu ta tabbatar masa da nasarar zaɓensa wanda ɗan takarar jam iyyar PDP Abba Kabir Yusif ke ƙalubalantar zaɓen da ya gudana.

A yau babbar kotun ƙoli ta yaɓke hukunci tare da yin watsi da ƙarar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: