
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano karkashin jagorancin Kwamishinanta *Cp Habu A. Sani, psc* na sanar da al’ummar Jihar kano cewa, *Hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC zata sake gudanar da zabuka Ranar Asabar 25/01/2020 a Kananan hukumomin Bebeji, Tudun Wada, Doguwa, Rogo, Kumbotso, Kiru, Bunkure, Minjibir da kuma Karamar Hukumar Madobi.*
Hukumar na bada tabbacin cewa *tayi hadin kai da takwarorin hukumomin tsaro dake nan Kano domin tabbatar da anyi zabe lafiya an kuma gama lafiya*,

A don haka, al’umma su tabbata sun kiyaye da:-

1. Duk wani motsin ababen hawa kamar Motoci, Adaidaita Sahu da Babura an haramta shi tun daga daren jajiberen ranar zaben har a kammala a wadannan kananan Hukumomi Guda Tara da za’ayi zabe, in banda motocin Asibiti, Jami’an Kashe Gobara, Ma’aikatan zabe da wadanda hukumar zaben ta tantance.
2. Ba’a yarda duk wasu matasa yan tada zaune tsaye su kusanci inda ake gudanar da zaben ba.
3. Daukar duk wani makami ko kuma abun cutarwa a yayin gudanar da zaben, jami’an tsaro ba za su amince da haka ba.
4. Iya wadanda suka cancanci zabe za’a bari a harabar zaben.
5. Duk wanda bashi da katin zabe da yake nuna lambar akwatin zabensa a wannan yanki, hukuma zatayi awon gaba dashi.
6. Bamu aminta da kawo wani mutum ko wasu mutane inda ake zaben ba. Matukar ba hukumar INEC ce ta tantance suba sannan iya wakilan Jam’iyyun da hukumar zabe ta tantance aka amince da zuwan su zaben.
7. Rundunar ‘Yan sanda ta Jihar Kano na yiwa al’umma fatan yin zabe lafiya kuma a gama lafiya.
Don neman taimakon gaggawa ko kuma sanar da faruwar wani lamari, sai a kira wadannan lambobin *08032419754, 09029292926, 08123821575*.
*Mungode da hadin kan da ake bamu*
*MAI SANARWA*
DSP ABDULLAHI HARUNA
KAKAKIN RUNDUNAR ‘YAN SANDAN JIHAR KANO
*AMADADIN KWAMISHINAN ‘YAN SANDAN JIHAR KANO*