Ministan Harkokin Noma, Sabo Nanono,ne ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta ciwo bashin dala biliyan Daya domin sawo kayan noma na zamani ta raba wa manoma.

Nanono ya yi wannan bayanin ranar Juma’a a Abuja a lokacin da ya ke kaddamar da kwamitin Shirin Inganta Noma na Green Imperative Programme.
Ya ce za a karbo bashin daga Bankin Kasar Jamus, Da Bankin cigaban Noma na kasar Brazil da kuma Bankin Musulunci, wato Islamic Development Bank.

Ministan ya ce an kulla yarjejeniyar biyan bashin nan da zuwa shekaru 15.

In dai aka karbo bashin dai kamar yadda Nanono ya bayyana, za a sayo kayan aikin noma ne domin a raba wa manoma a fadin kananan hukumomi 774 na fadin kasar nan.