Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana nasarar da aka samu a zaɓen cike gurbin da ya gabata a matsayin hujja mai ƙarfi da ya yiwa tsohon mai gidansa ritaya a siyasa.

Ganduje ya bayyana cewar ya yiwa kwankwaso ritaya a siyasa ganin yadda ƴan jam iyyar APC ne ke da nasara a zaɓen da ya gabata.
A yayin da shugaban majalisar dokokin jihar Kano ke gabatar da ƴan takarar majalisar da suka yi nasara a zaɓen da ya gabata, Ganduje ya ce lissafin siyasa ne ya kai ga matakin da yake kai a yanzu.

Ya ce a yanzu jam iyyar APC ce ke mulki tun daga sama har ƙasa, kuma tsarin da yake da shi ne ya sa shi matsayin da yake a ayanzu.

Yayin da ya bayyana Alhaji Musa Kwankwaso a matsayin mutum mai hazaƙa da kwazo don kawowa al ummarsa cigaba.
Gwamnan ya taya mahaifin kwankwaso murna wanda a kwanannan masarautar Bichi ta ɗaga likkafarsa a matsayin jerin mutanen da ka iya naɗa sarki.
Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana mahaifin kwankwaso a matsayin mutumin nagartacce wandazai kawo cigaba saboda jan mutane da yake a jiki.