Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Ba ni da hurumin shiga rikicin masarautun Kano – Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar ba shi da hurumin shiga rikicin masarautun Kano.

Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne yayin da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci sabbin ƴan majalisar wakilai da aka sake zaɓensu kwanakkin baya.

Ya ce kundin tsarin mulki bai baahi dama don shiga rikicin masarauta ba, haka kuma a kan tsarin yake sannan ba shi da ikon tsallaka iyaka.

“Majalisar dokokin Kano ce ke da hurumi ita doka ta sahalews shiga rikicin”Buhari.

Idan ba a manta ba ko da a baya shugaba Buhari ya taɓa wannan furuci yayin da rikicin ya yi tsami.

Kamar yadda ya faru batun masarauta a Kano ya faro ne tun kafin ƙara sabbin masarauru huɗu a jihar wanda ake ganin hakan na da alaƙa da siyasa.

Gwamnan Kano Ganduje ya gabatar da wasu nasarori da ya aiwatar a gwamnatinsa, cikin nasarorin akwai samar da kyamarar tsaro da ake sakawa a manyan titunan Kano, da kuma samar da filin horon sojoji a Kano.

An yi taron ne a yau juma a wanda sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero ya wakilci sauran sarakunan Kano.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: