Hukumar Dake lura da al’amuran wutar lantarki ta kasa NERC ta haramtawa kamfanonin rarraba wutar da adadinsu ya kai 11 karban kudin wuta a kowane wata da ya haura Naira dubu 1,800 daga abokan huldarsu a bangaren gidaje, har sai ta sa masu mita

Wannan ya biyo bayan yawan korafi da al’umma ke yi kan tsadar kudin wuta na kiyasi da kamfanonin rarraba wutar lantarki wato (DisCOs) ke yi a kan masu amfani da wuta
A wata sanarwa na umarni da hukumar ta fitar dake dauke da sa hannun shugabanta Farfesa James Momoh da Kwamishininta a bangaren dokoki, tabbatar da bin ka’ida da kuma bada lasisi Barista Dafe Akpeneye, hukumar ta NERC ta ce, ta soke dokar shekarar 2012 da ta baiwa kamfanonin damar sa kudin wuta kan tsarin kiyasi, sannan ta ce wannan dokar ta fara aiki tun a ranar Alhamis da ta gabata.
Alummata

