Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta tabbatar da ceto wata mata da ƴarda waɗanda aka yi garkuwa da su a daren jiya.

Ƴan bindiga sun shiga garin ƴan maiwa da ke ƙaramar hukumar Batsari ɗauke da muggan makamai har suka yi awon gaba da matan su biyu.
Ba tare da ɓata lokaci ba jami an ƴan sanda na kan kace kwabo suka yiwa dajin ƙawanya tare da musayar wuta har suka samu ceto mutane biyun da aka tafi da su.

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Gambo Isah ya ce har yanzu suna cigaba da farautar waɗanda suka tsere.
