Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi u kwankwaso ya bayyana cewar ya kamata ƴan ƙasa a haɗa kai a duƙufa don yiwa ƙasa addu a kan wannan annuba ta cutar sarƙewar numfashi wato Corona Virus.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam iyyar PDP da ya gudana.
Ya ce babban al amari ne ganin yadda duniya ta maida hankali a kan cutar wadda ke da saurin yaɗuwa.

Ya ƙara da cewa ya kamata gwamnati ta samar da hanyar da za ta ke koyar da ɗalibai karatu a gida ta hanyar murya ko faifan bidiyo yadda zai zamto ɗaliban suna karatu a gidajensu.
