Majalisar wakilai ta ce bata tunanin dakatar da zamanta a da ta saba yi sakamakon da barkewa annobar cutar Covid 19.

Mai magana da yawun majalisar wakilan, Banjamin Kalu ne ya bayyana haka a yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja a jiya.

A cewarsa Akwai ‘yan majalisu 360 a majalisar wakilan kasar da kuma dubban baki da ake samu duk mako.

Domin hana yaduwar annobar, tuni dai wasu gwamnatocin jihohi suka hana taron da ya fi na mutane 50.

Sai dai majalisar ta bakin Kalu ya ce yan majalisan za su ci gaba da zamansu domin samun damar sassaita zafafan batutuwa.

Muryan yanci ta Rawaito cewa Majalisar tace “akwai aiki a gaban su dan haka ba sa jin za su dakatar da zaman saboda cutar”.

Sai dai ya bayyana cewa idan har hakan ya zama dole nan gaba za ta fito ta sanar amma yanzu hakan ba zai sa su daina zama ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: