Gwamnatin jihar Kano ta bada umarnin rufe dukkan hanyoyin shige da fice na jihar Kano don rage yaɗuwar annobar Corona Virus

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana ranar juma a matsayin rana da za a rufe iyakokin shiga jihar baki ɗaya.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar Mallam Abba Anwar ya fitar a daren laraba.

Gwamnan ya ce ya zama wajibi a yi hakan don daƙile bullar cutar numfashi ta Corona Virus.

Ya ce duk da kasancewar matakin da gwamnatin ta ɗauka yana da tsauri amma hakan ya zama tilas domin tsare lafiya da dukiyoyin al umma.
Cikin jami an da za su saka ido don ganin an rufe ko ina akwai jami an ƴan sanda, da hukumar kula da tuƙi a Kano wato KAROTA sai hukumar Hizba.
Za a rufe ne tun daga ranar juma a da misalin ƙarfe 12 na dare.
Sannan gwamnan ya buƙaci al umma da su duƙufa da addu a tare da bin dukkan hanyoyin da masana kiwon lafiya suka bayar don gudun yaɗuwar cutar a faɗin jihar.