Gwamnatin tarayya ta musanta Labaran da ake yadawa a kafafen sada zumunta na cewa Gwamnatin tarayya zata bawa kowanne Dan Najeriya tallafin naira 30,000 don rage radadin wannan annoba da ya bulla ta Corona Virus.

Mataimaki na musamman shugaban kasa Muhammmad Buhari akan Kafafen yada labarai Mista Femi Adesina shine ya musantan wannan labarin a yau.

A cewarsa Labarai ya karade kafafen sada zumunta na zamani cewa Gwamnatin tarayya zata rabawa yan Najeriya sama da Miliyan 40 tallafin naira dubu 30 ga kowanne.

Wanda za’ayi amfani da lambobin BVN don raba tallafin.
Yace wannan labarin ne Mara tushe balle makama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: