Najeriya ta samu karin mutane 603 da suka kamu da cutar coronavirus, abinda ya sanya jimillar wadanda suka kamu da cutar a kasar kaiwa dubu 28 da 167, daga cikinsu kuma mutane 634 suka mutu.

Rahoton da hukumar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC ta wallafa a daren jiya asabar, yace an samu karin mutanen 603 ne a jihohi 18, kuma Legas ke kan gaba da adadin 135, sai Edo mai mutane 87, Abuja 73, yayinda aka samu sabbin kamuwa 67 a Rivers.

Inda suka samu waraka kuwa, an samu Karina mutane 393 gwaji ya tabbatar sun warke daga cutar ta coronavirus a jiya asabar, abinda ya sa jumillar adadin kaiwa dubu 11, da 462.

Leave a Reply

%d bloggers like this: