Rahotannin da Mujallar Matashiya Ke samu yanzu na cewa fadar shugaban kasa ta maye gurbin Ibrahim Magu da Muhammad Umar.

Muhammad shine babban daraktan gudanarwa na hukumar dake yaki da masu yiwa kasa zagon kasa EFCC, kuma shine zai kasance mukaddashin shugaban hukumar kamin daga bisani a nada Wanda zai jagoranci hukumar.

Tsohon Mukaddashin Ibrahim Magu ya shafe shekaru 5 yana jagorancin hukumar a matsayin mukaddashin shugaban hukumar. Sai a ‘yan kwanakin nan wasu tuhume tuhume suka taso akan wasu zargin da ministan shari’a ke masa na almundahanar wasu makudan kudade.

Leave a Reply

%d bloggers like this: