Sadiya Umar faruƙ ce ta bayyana hakan yayin gabatar da jawabi na kwamitin shugaban ƙasa kan cutar Covid 19.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewar, Ministar ayyukan jin ƙai ce ta bayyana hakan ranar Litinin.
Ta ce a Abuja an ciyar da gidaje sama da dubu ahirin da tara, sai legas da aka ciyar da mutane sama da dubu talatin da bakwai, sannan sama da gidaje dubu sittin sun ci gajiyar tsarin.

Sadiya ta kimanta kowanne kwanon abinci a naira 4,200.

Shugaba Muhhammadu Buhari ne ya bada umarnin ciyar da ɗalibai yayinda ma aikatarta suka tuntuɓi gwamnonin jihohi uku don cigaba da gudanar da tsarin na ciyar da ɗalibai a gida kuma suka amince
