A daidai lokacin da aka koma makaranta ga ɗaliban da za su rubuta jarrabawar fita daga sakadire.

Gwamnatin Kano ta sha alwashin korar duk wani shugaban makaranta da ya tsallake dodokin da aka gindaya don kariya daga Corona.

Kwamishinan ilimi na jihar Sunusi Ƙiru ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da yayi da BBC.

Ya ce babu shakka sai da aka cimma matsaya kafin bawa daliban damar komawa makarantu, kuma ba za su zuba ido a karya wannan doka ba.

Ya ƙara da cewa a matakin da ake a yanzu ya zama wajibi shugabannin makarantun su saka ido don ganin cewa an shawo kan matsalar.

Amincewar komawa makarantun da gwamnatin ta yi ga ɗaliban da suke ajin ƙarshe na babbar sakandire, an fara karatun ne a yau Litinin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: