Babbar kotun shari ar musulunci da ke ƙofar kudu ƙaeƙashin mai shari a Ibrahim Sarki Yola ta yanke hukuncin kisa ta hanyar jifa a kan wani tsoho bisa laifin fyaɗe.

Ƴar sanda a Kano sun kama Mati Audu tun a shekarar 2019 bisa aikata laifin fyaɗe ga yarinya mai shekaru 12 a duniya.
Mati Audu mai shekaru 60 a duniya an yanke masa hukuncin ne ƙarƙashin sashe na 127 (b).

Mutumin ya kasance mazaunin garin Farsa a ƙaramar hukumar tsanyawa.
