Mai dakin gwamnan jihar kaduna Hajiya Aisha El’Rufa’I , tayi kira da a ringa fallasa masu aikata laifin fyaɗe .

Hajiya Aisha tayi wannan kiran ne yayin wani gangami data jagoranta a kaduna sannan ta hori masu unguwanni da dagatai da su daina rufa asirin masu aikata laifin.
Haka kuma tace a ringa tabbatarwa ana hukunta duk wanda aka samu da cin zarafi musamman laifin aikata fyade.

Matsalar fyade tayi tsamari a najeriya cikin wannan shekara wanda hakan ke jawo wasu daga cikin wanda akaiwa fyade rasa rayukansu.
