Rundunar ƴan sandan jihar katsina ta tabbatar da kama mutane 40 waɗanda ake zargi da ƙona ofishin ƴan sanda.

Fusatattun mutanen da suka yi zanga zanga tare da rufe babban titin Jibia a Katsina, sun bankawa ofishin ƴan sanda da ke kan iyaka a yankin jibia.

Mai magana da yawun ƴan sanda a Katsina SP Gambo Isah ya tabbatar da cewar, ana zargin mutanen da lalata motocin ƴan sanda a yankin.

Ya ƙara da cewa kwamishinan ƴan sanda ne ne ya bada umarni ga ƴan sanda masu aikin kwantar da tarzoma don halartar wajen kuma aka shawo kan lamarin.

Sai dai ba a bayyana dalilin matasan na gudanar da zanga zangar ba, ko da yake a baya ƙungiyar kwadago ta shirya tsunduma yajin aiki a jiya litinin sakamakon ƙarin farashin man fetur da wutar lantarki.

Gambo Isah ya ce,suna nan suna gudanar da bincike a kan mutanen da ake zargi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: