Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Kuma dai – Ƴan bindiga sun hallaka mutane 14 a Katsina

Wasu da ake zargi ƴan bindiga ne sun kashe mutane 14 a jihar Katsina.

An hallaka mutane shida a ƙamar hukumar Faskari, sai mutane shida da aka sake kashewa a ƙauyen shau sai mutum biyu a garin garin ruwan godiya.

Ƴan bindigan sun shiga ƙauyukan da muggan makamai a kan Babura

Mai Magana da yawun ƴan sanda a jihar Kastina S.P Gambo Isa ya tabbatar da mutuwar mutane 8, sannan ya ce maharan sun gudu ne yayin da jami an tsaro suka isa garin.

Ya ƙara da cewa akwai mutanen da suka samu muggan raunuka a sanadiyyar harin kuma tuni aka kaisu asibiti.

Al amarin ya faru ne a ranar lahadi da daddare wayewar jiya litinin.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: