Mujallar Matashiya ta cika shekara huɗu da kafuwa, abubuwan da ya kamata ku sani a kanta

Mujallar Matashiya mujalla ce da ake wallafawa a takarda sau ɗaya a kowanne wata.

An samar da ita ne don haskawa al’umma hanyar da ɗalibai za su bi wajen amfani da ilimin da suke da shi don dogaro da kansu tare da samar da aikin yi a tsakanin matasa kasancewar wasu daga cikin matasan hankalinsu na karkata ga gwamnati don ganin ta sama musu aikin yi.

Kawar da zaman kashe wando tare da nusashe da al umma muhimmancin dogaro da kai shine tsarinta.
An fara wallafa mujallar Matashiya a watan Oktoban shekarar 2016, tare da manufar amfani da kuɗaɗen shiga don tallafawa matasa wajen sama musu aikin yi ta hanyar koya musu sana’a kyauta.
A watan Oktoba na shekarar 2017 mujallar Matashiya ta fara gabatar da shirye shirye na kallo a tare da amfani da yanar gizo a matsayin hanyar da za a cigaba da wallafa labarai kafin farkon wata da mujallar ke fita.
Cikin shekara ta 2017 ɗin dai kuma Mujallar Matashiya ta fara aikinta na cimma manufarta wajen koyawa matasa sana’a kyauta duk da cewa ba a samu hanyoyin kuɗaɗen da za a riƙeta har a samu rarar da za a yi amfani da shi wajen wancen ƙudiri ba.
A shekarar 2017 ɗin dai mujallar Matashiya ta horas da matasa 287 sana a kyauta, haka kuma aka yi bikin yaye mutanee 120 a shekarar.
Cikin shekarar 2018 kuwa Mujallar Matashiya ta horas da matasa sana’o i kamar Gyaran janareta, sarƙa da ɗan kunne, Ɗaukar Hoto mara motsi da mai motsi, da kwalliya wanda ta koyawa matasa 728, kuma aka yi bikin yaye matasa 300 a shekarar 2018.
Da kammala bikin yaye matasa 300 nee kuwa aka cigaba da bada dama wajen koyawa Matasa sana a a ƙarshen shekarar 2018 har shekarar 2019, sai dai ba a yi bikin yaye ko mutum guda a shekarar 2019 ba har aka shiga shekarar 2020 sai aka fitar da tsarin koyar da sana o i, sai dai ba a samu nasarar hakan ba sakamakon cutar Korona.
Lamarin da ya sa tilas aka dakatar har lokacin da aka samu sauƙin yaɗuwar cutar.
A watan Agustan shekarar 2020 ne aka sanar da bada damar cigaba da koyawa matasa sana a wanda a yanzu haka ake gab da bikin yaye wasu daga ciki.
A karon farko, Mujallar Matashiya ta horas da matasa aikin jarida kyauta don ganin an inganta hanyoyin sadarwar zamani cikin kwarewa.
Idan muka duba baya kaɗan a shekarar 2019 aka dakatar da wallafa mujallar takarda sakamakon harkokin karatu da suka koma kafafen sadarwar zamani na yanar gizo.
Sai dai an ƙarfafawa ɓangaren talabiji gwiwa don inganta hanyoyin sadarwar tare da tabbatar da gudanar da aikin cikin tsari da dokokin aikin jarida.
A halin yanzu a iya cewa Mujallar Matashiya ta cimma manufarta bisa la akari da yadda matasa suka zabura wajen dogaro da kansu.
Misalin gidajen jaridu na yannar gizo da sauran hanyoyin da matasa da sauran al umma ke bi don ganin sun ƙirƙirarwa kansu abin yi ba tare da dogaro da aikin gwamnati ba.
Abubakar Murtala Ibrahim
Shugaban Mujallar Matashiya