Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana ranar 8 da 9 ga watan Nuwamban da muke ciki a matsayin ranar da za a koma makarantu firamare da sakandire a faɗin jihar.

Kwamishinan ilimi na jihar Shehu Muhammad Maƙarfi ne ya bayyana hakan wanda y ace gwamnatin ta umarci malaman makarantun da su shirya karɓar ɗaliban makarantun kwana daga ranar 8 ga wAtan da muke ciki, yayin da makarantun jeka da za su koma ranar 9 ga watan.

Haka kuma sauran manyan makarantun gaba da sakadire ma za su koma daukar darasu daga ranar litinin mai zuwa.

Gwamnatin ta yi umarni da dukkan malaman makarantun da su kasance suna bin dukkan dokokin kariya daga kamuwa da cutan Korona.

Haka kuma ta yi umarni da shugabannin makarantun su kasance sun tsara dukkan hanyoyin kaucewa cutar a tsakanin dalibai

Kimanin watanni takwas makarantun suka kasance a kulle tun bayan ɓullar cutar Korona a Najeriya.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: