Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter, gwamnan jihar Naija Abubakar Sani Bello ya kamu da cutar Korona.

Bayan samunsa da cutar, gwamnan ya killace kansa kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana.
An yiwa gwamnan gwajin cutar kuma aka tabbatar yana ɗauke da ita kuma nan take ya killace kansa.

Idan ba a manta ba ko da a baya, sai da shugaban kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa don daƙile yaɗuwar cutar ya fitar cewa za a samu hauhawar mutanen da cutar za ta harba cikin makwanni biyu.

Ko da rahotannin da aka fitar a jiya, sai da aka samu ƙarin mutane 300 da cutar ta harba.