A mu hukunta duk wanda ya saka fim ko waƙa a youtube matuƙar bamu tantance ba ko a wanne gari yake – A cewar Afakallahu

Shugaban hukumar tace fina finai da ɗab i ta jihar Kano ya ce wajibi ne a kai musu duk wani fim ko waƙa su tantance kafin a sakeshi a Youtube.

Afakallahu ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da Mujallar Matashiya a yau Litinin.

Ya ce wajibi ne duk wanda yayi rijista da hukumar ya bi wannan doka ko a wanne gari yake ya bi dukkan dokokin hukumar tace fina finai don tsaftace sana ar.

Sannan kuma ya ce ba iya ƴan jihar Kano dokar ta tsaya ba, ya ce wajibi ne ga duk wani da yayi rijista da hukumar.

Kuma akwai hanyoyin da suka ware don hukunta waɗanda suka saki fim ko waƙa ba tare da an kai sun tace ba.

Guda cikin hanyoyin da za su bi na hukunta waɗanda ba a Kano suke ba shi ne haka kasuwancin fim ko waƙar a yanar gizo a dukkan faɗin jihar.

Afakallahu ya ce manufofi ne masu kyau da hukumar ta tanada don tsaftace masana antar shirya fina finai kuma abin alfahari ne ga jihar Kano kasancewar ita kadai ce ke da tsari a harkar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: