Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci neman afuwata daga jami’ar da aka yi amfani da sunanta wajen bashi muƙamin Farfesa.

A watan da ya gabata ne dai wasu da ke iƙirarin wakiltar jami’ar suka karrama gwamna Ganduje a matsayin farfesa a bisa gogewarsa wajen shugabanci na gari.

Bayan sanarwa ta fita, jami’ar  Carolina ta musanta lamarin wanda ya jawo cece-kuce a tsakanin jama’a.

Wani daga ɓagare a jami’ar ne ya jagoranci karrama gwamnan da sunan makarantar, kuma daga bisani suka musanta.

Cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin Kano Mallam Usman Alhaji ya fitar ya ce an yi hakan ne don ɓatanci ga gwamnatin.

Ya ƙara da cewa za a bi dukkan matakan da suka dace wajen ganin an hukunta waɗanda suka shirya lamarin.

Gwamnatin ta nuna takaici a bisa faruwar lamarin, kuma ta lashi takobin daƙile hakan a nan gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: