An cigaba da gudanar da zanga zangar ƙyamar ayyukan rushashshiyar rundunar sars a jihar Osun.

Dandazon matasa ne suka fito tare da tattaki zuwa majalisar dokokin jihar kuma suka buƙaci shugaban majalisar yay i musu jawabi.
Masu zanga zangar sun fito tare da bayyana halin matsi da ake ciki da buƙatar shugabanci na gari.

A ɓangare na jami an tsaro, mai Magana da yawun yan sanda a jihar Yemisi Opalola y ace rundunar yan sandan jihar na da masaniya a dangane da zanga zangar.

A wani labarin kuma shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yay i gargaɗi ga masu fakewa da zanga zanga wajen lalata duniya tare da sanadin asarar rayuka.
Shugaban yayi wannan gargaɗi ne a yayin wani taro da rundunar sojin najeriya ta shirya yau litinin.
Ya ce duk wanda aka samu da laifin tada zaune tsaye za a hukuntashi don tabbatar da doka da oda a faɗin ƙasar.
Sannan ya yabawa rundunar sojin a bisa gudunmawar da suka bayar wajen tabbatar da zaman lafiyta a jihohjin da aka samu hargitsi a yayin zanga zangar kyamar sars a wasu jihohin Najeriya.