Hukumar DSS a Najeriya ta ce akwai yuwar kai hare-haren ƙunar baƙin wake a yayin bikin kirsimeti a Najeriya.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Peter Afunanya ya fitar a daren jiya Talata.

Sanarwar ta ce ya kamata mutane su yi taka tsantsan da wuraren da za su je a yayin bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara.

Sanarwar ta ce ƴan ta’addan za su kai harin ne ta hanyar tada bama-bamai, da ƙunar bakin wake a wuraren da jama’a ke taruwa.

Hukumar ta buƙaci al’umma da su kai rahoton duk wani abu wanda ba su gamsu da shi ba a kan lokaci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: