Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce bisa kyakkyawar manufa gwamnatinsa ke cefanar da kadarorin gwamnati.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da ya kai ziyarar gani da ido kasuwar ɗan gwauro da ke kan titin zuwa Zaria a Kano, kamar yadda babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Mallam Abba Anwar ya bayyana.

Ya ce siyar da wuraren shi ne mafi alkhairi ga mutane  jihar Kano, domin zai haɓaka tattalin arziƙin jihar tare da samar da aikin yi a tsakanin mutanen  jihar.

Gwamna Ganduje ya ce gwamnatinsa za ta yi duk mai yuwuwa wajen kammala dukkan ayyukan da ta fara kafin wa’adinta ya cika.

Ganduje ya bayyana wasu wuraren da aka siyar a matsayin maɓoyar ɓata gari wanda ake amfani da su don yin ba daidai ba.

Wuraren da aka siyar waɗanda suka haɗa da Daula Hotel, filin ajiye ababen hawa na shahuci, gidan jaridan Triump da sauraren wurare daban daban.

Wasu daga al’ummar Kano na kallon hakan a matsayin wata hanya da gwamnatin ke kwashe kuɗaɗen al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: