Gwamna jihar Borno Babagana Zulum ne ya bayyana hakan a yayin da ya ziyarci hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa a Abuja.

Babagana Zulum ya buƙaci hukumar da ta tallafawa mutanen waɗanda rikincin tada ƙayar baya ya sa suka bar muhallinsu.
Zulum ya ce mutanen na ƙarƙashin garuwuwa 11 na jihar Borno.

Gwamnan ya nemi agaji daga hukumar hana fasa kwauri don ganin a tallafawa mabuƙatan kamar yadda ya ce, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin raba kayan abinci ga wurren da aka samu rikicin ƴan bindiga a ƙasar.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa a Najerira NEMA AVM Muhammadu Muhammad mai ritaya ya ce za su yi iya bakin ƙoƙarin su don ganin an tallafawa mabuƙata a jihar.
Sannan ya jinjinawa gwamna Zulum a bisa jajircewarsa wajen shugabancin al’umma