Aƙalla jarirai goma ne suka mutu yayin da wata gobara ta tashi a wani Asibiti da ke jihar Maharashta na ƙasar Indiya.

Gobarar ta faru ne wayewar garin hyau Asabar a sanadin wutar lantarki kamar yadda guda cikin ma’aikatan ta bayyana.
Mahukunta a asibitin sun ce bakwai daga cikin jariran hayaƙi ne ya kashe su yayin da uku daga ciki wutar ta yi ajalinsu.

Sannan an yi nasarar ceto wasu jariran da suka kuɓututa daga hatsarin gobarar.

Gwamnatin ƙasar ta bayar da umarnin bincike kan sanadin tashin gobarar tare da hada bayanai a kai.
Sannan za a bayar da diyya Rufi 500,000 ga iyayen jariran da suka halaka a sanadin gobarara a asibitin.