Shugaban ƙasar Najriya Muhammadu Buhari ya gargaɗi gwamnan Ondo bisa matakin korar makiyaya da suke cikin jihar.

Gwamnan Ondo ya bayar da wa’adin kamo guda ga makiyayan da suke cikin dazukan jihar da su fice daga ciki, a wani salo na magance muggan laifuka a jihar.

Sai dai fadar shugaban ƙasar ta mayar da martini cikin wani saƙo da babban mai taimakawa shugaban ƙasa a kan yaɗa labarai Mallam Garba Shehu ya fitar.

Sanarwar ta ce ya kamata a ɓagaren gwamnati da ɓangaren shugabannin Fulani su yi zama na ganin an shawo kan matsalar amma ba matakin da ya ɗauka na korarsu ba.

Sannan za su ci gaba da sa ido don ganin ko gwamnan zai ɗauki shawarar janye matakin nasa, idan bah aka ba kuwa za su ɗauki mataki na gaba.

A cewar shugaban ƙasar, Bai kamata a lokaci guda a kori dubban mutanen da suka shafe shekara da shekaru suna kiwo a jihar ba sakamakon ayyukan ɓata gari.

Sai dai gwamnatin jihar ta zargi fadar shugaban ƙasar da goyon bayan Fulani cikin wani martini da gwamnatin ta mayarwa fadar shugaban ƙasa.

Kamar yadda kwamishinan yada labarai a jihar Ondo Donald Ojogo ya ce kalaman fadar shugaban ƙasar na iya haifar da matsala a ƙasar.

A ƙarshen makon da ya gabata ne dai gwamnan  jihar Ondo ya bada umarnin ga makiyayan da su fiye daga dukkan dazukan jihar zuwa ranar Lahadi mai zuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: